Masu fafutukar neman shugabancin hukumar kwallon kafar Najeriya.

Win money on DrumbeatNews !!!

A yau Alhamis mutum daya cikin hudu masu takara ne zai zama shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF).
An shirya gudanar da zaben a birnin Katsina da ke arewacin Najeriya, kuma duk da yunkurin da wasu ke yi na dakatar da zaben, ana sa ran komai zai wakana kamar yadda aka tsara.
Wani tsagi na hukumar da ke ikirarin gudanar da wata kungiya mai kula da harkokin ‘yan wasan kwallo ‘yan asalin Najeriya sun so su dakatar da zaben, kuma ministan wasannin Najeriya ya soki taron zaben inda ya kira shi ‘haramtacce’.
Amma hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta amince da a gudanar da zaben, har ta aika da Luca Piazza da Solomon Mudege a matsayin masu sa ido.
Shi kuma shugaban hukumar kwallon kafa ta Burkina Faso, Sita Sangare, zai jagoranci zaben a madadin hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika, wato CAF.
Mutanen da za su fafata a wannan zaben sune: Amaju Pinnick, wanda shi ne shugaban kungiyar mai ci, sai kuma Aminu Maigari wanda tsohon shugaban kungiyar ne. Akwai kuma Taiwo Ogunjobi da Chinedu Okoye.
Za a kuma zabi mambobin kwamitin gudanarwa da za su tafiyar da hukumar kwallon kafar ta Najeriya zuwa shekara ta 2022.
Amaji Pinnick
Ba a taba samun shugaban da ya yi tazarce ba a hukumar ta NFF, amma Amaju Pinnick na fatan shi ne wanda zai kafa tarihi a yau.
Aminu Maigari
Shi kuwa Aminu Maigari yana fatan komawa kan mukamin da ya bari ne a 2014, kuma yana da farin jini sosai a arewacin Najeriya.
Ya rike mukamin shugaban hukumar daga 2010 har zuwa 2014 a lokacin da rigingimu suka sa hukumar FIFA ta kori Najeriya daga buga wasanni bayan gasar cin kofin duniya da aka yi a Brazil.
Taiwo Ogunjobi
Akwai kuma tsohon sakatare-janar na hukumar, Taiwo Ogunjobi, wanda ya shafe fiye da shekara 20 yana tafiyar da harkokin kwallon kafa a Najeriya.
Ya rike mukamin sakataren hukumar daga 2002 zuwa 2005, kuma mamba ne na kwamitin koli na hukumar NFF daga 2005 zuwa 2010.
Chinedu Okoye
Daga karshe akwai Chinedu Okoye, wanda shi ne mutum daya da bai taba rike wani mukami a hukumar ba.
Shi ne shugaban kungiyar kwallon kafa ta Bimo Sporting Club da a yanzu ke buga wasanninta a rukuni na biyu na gasar Firimiyar Najeriya.
Okoye tsohon alkalin wasan kwallon kafa ne a Switzerland, kuma ya yi fice sosai a lokacin da ya ce cin hanci da rashawa sun mamaye gasar Firimiyar Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here