Mark Zuckerberg zai bayyana a gaban Kwamitin Amuruka don Amsa tambayoyi kan Bayanan Sirrin Masu amfani da Shafin

Win money on DrumbeatNews !!!

Mai kamfanin sada zumunta na Facebook Mark Zuckerberg, zai bayyana a gaban wani kwamitin majalisar zartaswa na Amuruka (US) don amsa tambayoyi kan abinda ya shafi tsarin adana surruka na kafar ta Facebook.

Kwamitin makamashin gidaje da Kasuwanci ya fitar da sanarwar cewa shugaban kafanin na Facebook zai bayyana a gaban kwamitin a ranar Laraba 11 ga watan Afrelu “dangane da tsarin adana bayanan surrukan masu amfani da kafar”

Kamfanin sada zumunta na Facenbook na ci gaba da fuskantar bincike daga mahukuntan kasar Amuruka, Burtaniya da kuma hadakar kasashen Turai (EU) bisa wani rahoto kan rikicin wani bayani tsakanin kamfanin na Facebook da kamfanin tuntuba na Cambridge Analytica.

Biyo bayanin zargin da kamfanin Facebook yayi na cewar kamfanin Cambridge Analytica ya saci bayanan masu amfani da shafin sada zumuntar, an bukaci manyan shuwagabannin kamfanin dasu bayyana a gaban majalisar zartaswa ta Burtaniya da kuma Kwamitin Majalisar zartaswa na Amuruka.

Mr Zuckerberg ya amsa gayyatar kasar Amuruka, kamar yadda kwamitin ya tabbatar, inda ya bayyana cewa:

“Wannan zaman zai taimaka wajen samun karin haske kan abinda ya shafi bayanan surruka na masu amfani da kafar sada zumuntar da zai taimakwa duk dan amuruka sanin ainihin halin da bayanansu yake a kafar ta Facebook.”

“Mun godewa Zuckerberg bisa ra’ayinsa na bayyana a gaban kwamitin, kuma muna tsumayin zuwansa don amsa mana tambayoyin da muka shirya masa a ranar 11 ga watan Afrelu.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here