Majalisar Ministoci Ta Amince Da Karin Bilyan 80 Don Aikin Hanyar Legas Zuwa Ibadan

Win money on DrumbeatNews !!!

 

A zaman majalisar ministoci na wannan mako a karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osibanjo, majalisar ta amince da kashe karin Naira Bilyan 80 wajen aikin hanyar Legas zuwa Ibadan.

Da yake karin haske kan zaman majalisar, Ministan Ayyuka da Hasken Wutar Lantarki, Babatunde Fashola ya nuna cewa tun da farko an kasafta Naira Bilyan 96.5 don aikin hanyar amma kuma sakamakon wasu canje canje da aka yi akan taswirar hanyar, shi ya janyo aka kara yawan kudaden da za a kashe don kammala aikin hanyar.

Haka ma, Ministan ya kara da cewa majalisar ministocin ta kuma amince da kashe Naira Bilyan 18.87 don gyara Babbar gadan nan ta ” Third Mainland” da ke cikin birnin Legas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here