Majalisar Dinkin Duniya Ta Janye Jami’anta Daga Yankin Rann

Win money on DrumbeatNews !!!

Sakamakon harin da ‘yan Boko Haram suka kai a garin Rann dake cikin jihar Borno,inda harin ya janyo mutuwar ma’aikara uku na Majalisar Dinkin Duniya, Sakatare Janar na António Guterres ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya data cafko tare da hukumta wadanda suke da hannu a harin don a hukunta su.

Guterres ya kuma tabbatar da kwashe daukacin ma’aikatan ajaji naMajalisar da kuma dakatar da ayyukan ta na wucin gadi data tura su yankin na Rann.

Sakataren ya yi tir da kashe jami’an a harin da aka kai masu a ranar Alhamis din makon da ya gabata.

Ya yi nuni da cewa, hare-haren da aka kaiwa al’umma da kuma kayan Majalisar, wanda yace, hakan ya sabawa dokar kasa da kasa ta kare ‘yancin adam. A cewar sa, “ wadanda suka aikata ta’asar a kasar nan, da sauran ta’asa dole ne a cafko don ayi masu hukunci.”

Sakataren ya yi kira ga zaukacin bangarorin biyu dasu tabbatar da cewar ako wanne lokaci suna bai wa al’ummar dake yanki kariya.

A cewar Sakataren ya bayyana cewar,daya daga cikin ma’aikatan ya samu mummunan rauni kuma har yanzu ba’a ga ma’aikatan Majalisar uku ba an kuma kashe jami’an tsaro takwas na Nijeriya.

Yace, “a lokacin harin samada ma’aikatan Majalisar arba’in da aka turasu garin Rann an hallaka su.” Sakataren ya sanar da cewa, dukkan ma’aikatan Majalisar da aka tura su garin Rann kuma an dakatar da ayyukan jin kai a yankin na wucin gadi.

Ya yi ta’aziyya ga iyalan ma’aikatan da da harin ya rutsa dasu da gwamnatin Nijeriya da kuma al’ummar kasar. Sakataren ya kuma yi fatan samun lafiya ga wadanda suka samu raunukan sakamakon harin.

A wata sabuwa kuwa, sananniyar kungiyar da Likitoci da basu da iyaka,ita ta dakatar da ayyukan ta na taimakawa a garin na Rann.

A cewar kungiyar, ta bayyana cewar ta baro marasa lafiya harda yara sittin a garin wadanda a yanzu kungiyar ta sanya su a cikin shirin ta na samar da abinci mai gina jiki ba tare da wani magani ba.

Kungiyar wadda ba dan neman kudi aka kafata ba, ta bayyana cewar ta kwashe ma’aikatan ta ashirin na kasar nan dana kasar waje daga garin.

A sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Asabar din data gabata ta samu sa hannu Manajan ta na sashen yada labarai Maro Berli. Sai dai, har yanzu ba’a san takamai mai mutane nawa ne aka kashe ba amma ma’aikatan kiwon lafiya a garin, sun yiwa mutane tara magani.”

Itama janmiyyar  PDP mai adawa, ta yi tir da kisan ma’aikatan,indatace Majalisar ta Dinkin Duniya data dora alhakkin kisan akan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.  Jamiyyar a sanarwar data fitar wadda Sakataren yada labarai na kasa Mist Kola Ologbondiyan ya fitar a ranar Asabar data gabata ya nuna alhinin sa akan kisan ma’akatan.

Bugu da kari, Shugaban Majalisar Wakilai ta kasa Mista Yakubu Dogara a sanarwar da ya fitar ranar Asabar data gabata ya yi tir da kashe ma’aikatan a garin na Rann. Dogara yace, harin ya shafi rayuka, inda ya danganta harin a  Shugaban Majalisar a karshe yace,“harin abin takaici ne ganin cewar ma’aikatan wanda suka sadaukar da rayukan su na bayar da agaji ace an kashe su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here