Magoya Bayan Jubentus Sun Kwashe Tsawon Minti 90 Suna Zagina – Mourinho

Win money on DrumbeatNews !!!

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho, ya bayyana cewa baiga laifin da yayiwa magoya bayan Jubentus ba akan murnar daya nuna bayan kungiyarsa tasamu nasara a gidan na Jubentus daci 2-1 a ranar Larabar.

Kungiyar Jubentus ce dai tasamu nasarar zura kwallo a raga ta hannun tsohon dan wasan Manchester United din Ronaldo sai dai daga baya Juan Mata ya farkewa United din yayinda daga baya kuma Aled Sandro yaci gida da kansa. Wannan ne karo na farko da Jubentus tayi rashin nasara a wannan kakar wasan kuma a gida a wasanninta na siriya A da kuma na zakarun turai kuma har yanzu itace ta farko acikin rukunin na sun a H. “Minti 90 sukayi suna zagina kuma babu abinda nace domin ni abinda yakawo ni shine inzo kuma in samu nasara kuma nasamu amma nayi hakane domin in nuna musu cewa banajin zagin da sukemin su kara karfin murya” in ji Mourinho Yaci gaba da cewa “Abinda nayi bai kamata ba sai dai sune suka jawo sun zagi iyalaina ma gida sannan sun zagin iyalina na Inter Millan saboda haka yakamata in rama amma da basu zageni ba babu ruwana dasu” Mourinho yace daman tunda yayi rashin nasara a hannunsu a gida ya shirya cewa shima sai yazo gidansu yabasu matsala kamar yadda suka bashi agaban magoya bayansa kuma shima ya rama saboda haka yanzu duk daya A karshe Mourinho ya yabawa dan wasa Mata da kwallon daya zura a raga ta bugun tazara sannan ya jinjinawa Maroune Fellaini bisa shigowarsa wasan kuma ya canja tunanin kowa a wasan kamar yadda kowa yagani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here