Ma’aikata Za Su Yi Yajin Aiki Sakamakon Komawar Ronaldo Jubentus

Win money on DrumbeatNews !!!

Rahotanni dagakasar Italiya sun bayyana cewa ma’aikatan kamfanin Fiat Chrysler plant zasu shiga wani yajin aikin sai baba ta gani sakamakon siyan dan wasa Cristiano Ronaldo da kungiyar tayi a wannan satin.

An bayyana cewa dai duka kamfanin na Fiat Chrysler plant da kungiyar Jubentus mallakin mutum daya ne wato iyalan Agnelli sai dai ma’aikatan kamfanin sun bayyana cewa zaifi kyau ace kungiyar ta zuba kudin a kamfanin maimakon ta siyi dan wasa guda daya. Ronaldo dai yakoma kungiyar kwallon kafa ta Jubentus ne a wannan satin dayake wucewa daga Real Madrid akan kudi kusan fam miliyan 100 kuma zai dinga karbar albashin kusan fan dubu dari biyar a duk sati. Ma’aikatan dai sun bayyana cewa yakamata kamfanin ya sakawa ma’aikatan kamfanin ta hanyar kara jari a kamfanin maimakon siyan dan wasa guda daya sannan kuma ya kamata kamfanin ya duba irin sadaukarwar da ma’aikatan sukewa kamfanin.

Yajin aikin dai zai fara daga ranar Asabar kuma zai kai har ranar Talata anayi a garin Melfi plant dake arewacin birnin Turin yayinda kuma dubban ma’aikatan kamfanin sukayi alkawarin fitowa domin yin yajin aikin. Ana saran ranar Litinin Ronaldo zai sauka a birnin Turin domin a gwada lafiyarsa a kungiyar sannan kuma ya saka hannu na tsawon shekaru hudu kafin kuma da yammacin ranar kungiyar ta gabatar dashi a gaban dubban magoya bayanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here