Likafa ta cigaba Masarautar Kano Za Ta Yi Wa Nazir M Ahmad Nadin Sarauta

Win money on DrumbeatNews !!!

Masarautar Kano ta fitar da sanarwar shirye-shiryen da take na yi wa sanannen mawayakin Hausa, Nazir M Ahmad, nadin sarautar “Sarkin Maiwakar Sarkin Kano”, Malam Muhammadu Sanusi na biyu.
Sanarwar nadin sarautar ta fito daga jawabin da shugaban ma’aikatan Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi, Alhaji Munir Sanusi ya damka wa kamfanin dillancin labaran Nijeriya, NAN, a ranar Lahadi.

Jawabin ya yi yabo ga Nazir M. Ahmad kan matsananciyar soyayyar da yake nuna wa ga Sarki da masarautar Kano tun ma Mai Martaba Sarkin yana matsayin Dan Majen Kano.

Jawabin ya kuma yi umarni ga Nazir da ya je ya samu shugaban ma’aikatan Sarkin domin su kammala tsare-tsare na ranar nadin sarautar.

Daga Wakilinmu Yaseer Kallah

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here