Kungiyar MASSOB ta ‘yan kabilar Igbo ta yi babban gargadi ga gwamnatin shugaba Buhari

Win money on DrumbeatNews !!!

Kungiyar Fafutukar Tabbatar da Kasar Biyafara wato MASSOB, ta gargadi gwamnatin tarayya ta daina cin mutumcin iyalan Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, musamman matar sa Patience. Kungiyar ta yi wannan gargadi ne a ranar Juma’a ta bakin Shugabanta, Uchenna Madu.

Madu ya ce, ba komai Jonathan ke fuskanta ba illa bita da kulli da wannan gwamnatin ke yi masa a kokarinta na zubar ma sa da mutumci. Ya kuma ce Gwamnatin ta na son disashe hasken tauraruwar Patience ne saboda irin goyon bayan da ta ke yi wa mijin na ta a siyasance.

A cewar Madu, Gwamnatin ta na tunanin idan ta garkame Patience to lallai siyasar mijin na ta zai durkushe. Ya kuma ce kasancewar Patience ‘yar kabilar Igbo ce, tozarcin da ta ke fuskanta ba komai ba ne illa tsabar kiyayya ga ‘yan kabilar da Gwamnatin Buhari ke yi.

KU KARANTA: Shugaban makarantar Sakandire da wasu malamai biyu sun shiga garari saboda dukan dalibai

Ya kara da cewa, akwai masu rike da mukamai a wannan Gwamnatin da dama wadanda su ke wasan kura da dukiyar al’umma, amma ko kadan ba a taba bincikar su ba. Haka zalika ba Patience ce kadai daga cikin Tsaffin Matan Shuwagabannin Kasa da su ka barnatar da kudin Kasa ba.

Don haka ne ya yi kira ga ‘yan kabilar Igbo da su cire tsoro a ran su, su tsaya tsayin daka don kare ‘yan uwan su. Najeriya Kasa ce a suna kawai, in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here