Kungiyar IS sun kai hari kan sojojin Amurka.

Win money on DrumbeatNews !!!

Kungiyar IS ta dauki alhakin wani hari akan wani ayarin sojojin Amurka da na wata kungiyar mayaka ta Kurdawan Syria a yankin Hasaka da ke arewa maso gabashin kasar.
A sanadiyyar wannan harin, sojoji 15 sun rasa rayukansu, inda wasu 25 kuma suka jikkata.
A wani sako da kungiyar ta IS ta fitar a shafinta na manhajar sadarwa ta Telegram a jiya Laraba, kungiyar ta ce mayakanta sun kai wani harin bazata kan wani ayarin hadin kai na dakarun Amurka da kungiyar UDF ta Kurdawa.
Sanarwar ta kuma ce ayarin sojojin da suka kai wa harin na cikin wasu motoci masu sulke guda 30 ne, kuma harin ya auku ne a unguwar Ghuwairan na birnin Hasaka.
Bayan kungiyar ta tayar da wasu bama-bamai, wadanda halaka dakarun Amurka da na Kurdawan, amma akwai alamar ayarin sojojin sun sami sukunin bude wuta na fiye da sa’a guda kafin aka kai masu dauki.
Kungiyar IS ta kuma yi ikirarin cewa ta kashe sojoji 40 wadanda a cikinsu akwai Amurkawa da Kurdawa, amma ba ta iya fadin yawan Amurkawan da suka mutu ba.
Amma kawo yanzu ba a sami wani martani daga bangaren dakarun Amurka da na Kurdawa ba.
Da alama dai kungiyar ta IS na kokarin farfadowa ne bayan da aka fatattake ta a Iraki, domin wanna ne karo na biyu da ta kai irin wannan harin a kasa da mako biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here