Ku zargi dillalai bisa wahalar man fetur – Jam’iyyar APC

Win money on DrumbeatNews !!!

Jam’iyyar APC ta ce wahalar man fetur da ake fuskanta a Najeriya ba laifin gwamnatin ta bane tare da bayyana cewar wasu ‘yan dillalai na boye man da gan-gan domin kawai su shafawa jam’iyyar bakin fenti.

A ranar Juma’a, jam’iyyar mai mulki ta bayyana cewar dillalan man fetur be suka haddasa wahalar man saboda hadamar samun kazamar riba.

Jawabin da jam’iyyar ta fitar a dandalin sada zumunta na Tuwita ya ce; “A gwamnatance babu wahalar man fetur. Wasu masu ruwa da tsaki a harkokin man fetur sun boye adadin da hukuma ke rabawa dillalan man saboda hadama.”

Layi a gidajen man fetur

Hakazalika jam’iyyar ta ce tana aiki tukuru domin shawo kan wannan matsalar.
Rahotanni sun bayyana cewar wahalar man fetur na kara ta’azzara a manyan biranen Najeriya.

KU KARANTA: Hotuna: Anyi taron gangamin neman Buhari ya kara tsayawa takara a jihar Kogi

A jihar Anambra ana sayar da man a kan farashin N250 da N300 a kan kowacce lita duk da hukumar DPR na kewayen gidajen mai domin tabbatar da an sayar a kan farashin gwamnati na N145 duk lita. Hukumar ta rufe gidajen wasu gidajen mai ciki harda wani gidan mai mallakar NNPC saboda sayar da man fiye da farashin gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here