Ku yi la’akari da damuwar tsaron Turkiyya, Erdogan ya fadawa duniya

Win money on DrumbeatNews !!!

Shugaban kasar Turkiyya ya yi kira ga kasashen duniya da su mutunta damuwar tsaron da Turkiyya ke fuskanta su kuma goyi bayan shirinta domin mayar da ‘yan gudun hijirar Siriya kasarsu

 

Shugaban kasar Turkiyya ya yi kira ga kasashen duniya da su mutunta damuwar tsaron da Turkiyya ke fuskanta su kuma goyi bayan shirinta domin mayar da ‘yan gudun hijirar Siriya kasarsu.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi jawabi a wani taro da wasu jami’an kungiyar kwallon kafa inda ya bayyana cewa “idan har duniya bata goyi bayan shirinmu na mayar da ‘yan gudun hijirar Siriya kasarsu ba toh ko shakka babu zamu bude kofofin iyakokinmu da Nahiyar Turai”

A yayinda ya nanata niyar Turkiyya na samar da yankin lumana domin hana kungiyar YPG/PKK da Daesh kai farmakin ta’ddanci daga Siriya ya tabbatar da cewa mun cimma kusan dukkan burinmu”

Erdogan ya kuma nanata wa’adin da aka baiwa ‘yan ta’ddar YPG/PKK domin su fice daga yankin arewacin Siriya.

Idan har ba’a kauda ‘yan ta’dda a arewacin Siriya cikin sa’o’i 150 ba toh Turkiyya zata kauda su ita tilo.

A ranar Talata ne dai Ankara da Moscow suka cimma matsaya a wata yarjejeniya wacce kungiyar ta’addar YPG/PKK zasu janye na kilomita 30 daga yammacin iyakokin Turkiyya da Siriya cikin awanni 150 daga bisani kuma dakarun Turkiyya da Rasha su dinga sintiri a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here