Kim Jong-un: Na shirya tsaf domin sake ganawa da Trump

Win money on DrumbeatNews !!!

Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya bayyana cewa ya shirya tsaf domin ganawa da shugaban kasar Amurka Donald Trump karo na uku domin yin sulhun diflomaasiyyar tsakanin kasashen biyu.

 

Kim Jong-un: Na shirya tsaf domin sake ganawa da Trump

Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya bayyana cewa ya shirya tsaf domin ganawa da shugaban kasar Amurka Donald Trump karo na uku domin yin sulhun diflomaasiyyar tsakanin kasashen biyu.

Kamar yadda kanfanin dillsncin labaran kasar Koriya ta Arewa KCNA ta rawaito shugaba Kim a yayinda yake jawabi a gaban majalisar kasarsa ya tabbatar da cewa a shirye yake domin sake ganawa da shugaba Trump a karshen shekara idan har Amurka ta amice da haka.

Kim da yake jaddada cewa, rashin daidaituwa game da kawar da makaman nukiliya da takunkumi na iya warwarew, ya kara da cewa:

“Idan har Amurka ta bi hanyar da ta dace bisa ka’,ida da daidaito, a shirye nake domin ganawa da Trump karo na uku. Ba zamu ki rataba hannu akan yarjejeniyoyin da zasu kare ra’ayoyin kasashen biyu ba, wannan gabadayarsa ya rataya ne akan wuyar Amurka”

Kim ya kara jaddada cewa taron da suka zauna da Trump na baya-bayan nan ya sanya shakku a zukata akan yiwuwar tabbatar da sulhu bisa kauna da adalci a tsakanin kasashen biyu.

Amurka ta kafa kaddamar da yarjejeniyar a bisa tubali maras daidaito. Basu kuma shiryawa a zauna akan tuburi domin warware matsalolin ba, mu muna bukatar a zauna domin warware matsalolin akan hanyar diflomasiyya, ba wai yadda Amurka take bukata ba. Bama bukatar sake irin zaman sulhun Hanoi inji Kim.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here