Katar ta sanar da za ta fice daga Kungiyar Kasashe Masu Fitar da Albarkatun Man Fetur (OPEC)

Win money on DrumbeatNews !!!

Katar ta sanar da cewa, daga ranar 19 ga watan Janairun 2019 ta fita daga Kungiyar Kasashe Masu Fitar da Albarkatun Man Fetur (OPEC).

Katar ta sanar da za ta fice daga Kungiyar Kasashe Masu Fitar da Albarkatun Man Fetur (OPEC)

Katar ta sanar da cewa, daga ranar 19 ga watan Janairun 2019 ta fita daga Kungiyar Kasashe Masu Fitar da Albarkatun Man Fetur (OPEC).

Ministan Ma’aikatar Makamashi ta Katar Saad Al-Ka’abi ya bayyana cewar Kasarsa kamar sauran kasashe za ta yi kasuwancin man fetur, kuma za ci gaba da aikin da alkawari da ka’idojojin Kungiyar Kasashe Masu Fitar da Albarkatun Man Fetur (OPEC) ne kawai nan da ranar 19 ga watan Janairun shekarar 2019.

Ministan Makamashin na Katar da ya sanar da ficewar kasarsa daga Kungiyar Kasashe Masu Fitar da Albarkatun Man Fetur (OPEC) ya ce “Daga Watan Janairu za mu kammala fice wa daga OPEC. A safiyae ranar Litinin din nan mun mika wa uwar Kungiyar matakin da muka dauka. Za mu ci gaba da aiki kamar sauran kasashe da ba mambobin OPEC ba wajen saya da sayar da man fetur a kasuwannin duniya.”

Al-Ka’abi ya ci gaba da cewar ficewar Katar daga Kungiyar Kasashe Masu Fitar da Albarkatun Man Fetur (OPEC) ba zai yi wani tasiri da yawa kan aiyukan Kungiyar ba, kuma fitar su daga cikinta bayan shekaru 57 ba abu ne mai sauki ba.”

Bayan bayar da wannan sanarwa da Katar ta yi za a gudanar da taro a ranar 6 ga watan Disamba.

Bayan wannan sanarwa da Katar ta fitar farashin man fetur ya karu da kaso 5 cikin 100.

A safiyar Litinin din nan an sayar da man samfurin Brent kan kudi dalar Amurka 62.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here