Mutane 19 ne suka rasa rayukansu sakamakon kifewar wani jirgin ruwan kwale-kwale a arewacin Najeriya.

Mutane 19 ne suka rasa rayukansu sakamakon kifewar wani jirgin ruwan kwale-kwale a arewacin Najeriya.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya bayyana cewa, jirign da ya kife a kogin Niger na dauke da fasinjoji 21 inda mutane 19 da suka hada da yara kanana suka mutu.
An bayyana cewar a bincike da aikin ceto da aka yi an kubutar da yara kanana 2.
A gefe guda kuma kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kwara Ajayi Okasanmi ya bayyana cewa jirgin ruwan ya dauki mutane sama da ka’ida.
A lokacinda ake samun mamakon ruwan sama a Najeriya, hatsarin jiragen ruwa na afkuwa a kogunan kasar.