Jirgi mai saukar ungulu ya kashe mutane uku a Sudan

Win money on DrumbeatNews !!!

An bayyana cewar faɗowar wani jirgi mallaƙar ƙasar Ethiopia dake sintirin samar da zaman lafiya a Sudan ƙarƙashin jagorancin Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku da raunanan wasu ukun kuma.

Jirgi mai saukar ungulu ya kashe mutane uku a Sudan

An bayyana cewar faɗowar wani jirgi mallaƙar ƙasar Ethiopia dake sintirin samar da zaman lafiya a Sudan ƙarƙashin jagorancin Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku da raunanan wasu ukun kuma.

Hukumar Samar da zaman lafiya a lyakokin Sudan da Sudan ta Kudu ta bayyana cewar jirgin yaki mai saukar ungulu kirar Mi-18 dauke da mutane 23 ya faɗo a yankin Abyei dake ƙasar Sudan.

Lamarin dai ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku da kuma samun munanan raunukan mutane uku da kuma raunanan wasu goma daga cikinsu.

Sanarwar ta bayyana cewar jirgin mai saukar ungulu da ya faɗo a yayinda yake shawagi daga jihar Kurdufan ta ƙasar Sudan zuwa Abyei dake yankin Sudan ta Kudu na dauke da sojojin kasar Ethiopia

Kawo yanzu dai ba’a bayyana dalilin faɗowar jirgin ba.

Ma’aikatan ƙasar Ethiopia dubu hudu da 500 ne ke ayyukan samar da zaman lafiya a Sudan.

Ƙasashen Sudan da Sudan ta Kudu na bayyana yankin Abyei mai dinbin arzikin man fetur a matsayin nasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here