Jigo a jam’iyyar PDP ya shigar da Atiku kara gaban kotu

Win money on DrumbeatNews !!!

Wani jigo a jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimaki na musamman ga tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar, kuma dan Jihar Adamawa, Dr. Umar Ardo, ya maka Atiku kara gaban kotu.
Dr. Ardo ya yi karar Atiku ne bisa zargin sa da amfani da kudi domin saye shugabancin Jam’iyyar PDP a jihar Adamawa, tare da bayyana yadda Atiku ke amfani da kudi wajen juya akalar zaben shugabannin jam’iyyar da aka gudanar a jihar.
A wasikar da ya aikewa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Ahmed Makarfi, Dr. Ardo ya nemi shugabancin jam’iyyar da ya rushe zaben da jam’iyyar ta gudanar a jihar Adamawa.
‘Yan jam’iyyar PDP na ganin Atiku Abubakar na yi ma su katsalandan cikin harkokin jam’iyyar ta su duk da kasancewar da dan jam’iyyar APC a halin yanzu. An dade dai ana yada jita-jitar cewar Atiku na tunanin kara komawa tsohuwar jam’iyyar ta sa matukar za su ba shi takarar shugabancin kasa a zaben 2019.

Atiku Abubakar

Saidai mataimakin na musamman ga Atiku a bangaren yada labarai, Paul Ibe, ya musanta wannan zargi da ake yi wa maigidan na sa, tare da bayyana cewar ma su zargin na yi ne kawai saboda sun rasa makama biyo bayan rashin nasarar wadanda suke so.
Dr. Ardo dai na zargin Atiku ya saye zaben wasu kananun hukumomi domin ganin ya dasa yaron sa a shugabancin jam’iyyar.

KU DUBA:Buhari ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2018 ga majalisar kasa

Ba a gudanar da zabe a kananun hukumomin Toungo, Ganye Mayo Belwa, Demsa, Numan, Shelleng, Yola ta Arewa, Yola ta Kudu, Mubi ta Kudu, Michika da Madagali“. Inji Dr. Ardo, zargin da Atiku ya yi watsi da shi a matsayin maras tushe balle makama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here