Isra’ila: Layin dogo, gayyata ce ta zaman lafiya

Win money on DrumbeatNews !!!

Ministan sufuri da na leken asiri na azzalumar kasar Isra’ila,Yisrael Katz ya ce batun gina layin dogon daga Isra’ila zuwa Saudiyya sahihi ne,kuma sun yanke wannan shawarar da zummar zama kalau da Larabawa.

 

Isra'ila: Layin dogo, gayyata ce ta zaman lafiya

Ministan sufuri da na leken asiri na azzalumar kasar Isra’ila,Yisrael Katz ya ce batun gina layin dogon daga Isra’ila zuwa Saudiyya sahihi ne,kuma sun yanke wannan shawarar da zummar zama kalau da Larabawa.

A cewar babban ofishin sadarwa na kasar Yahudu, MAKAN, Katz ya furta wannan kalamin a babban taron kasa da kasa kan sufuri wanda aka shirya a kasar Umman,inda ya ce:

“Wannan wani gaggarumin shiri ne mai matukar muhimmanci wanda ba shi da wata alaka da siyasa ko kuma yaduwar wasu akidoji.Donald Trump ma ya yaba wannan matakin da muka dauka.Saboda hanyar za ta zama tamkar gada tsakanin Turai da Isra’ila,kuma Jordan ce cibiya”.

Minista Katz ya kara da cewa,za a samar da layin dogon don sauwake sufuri da kuma kasuwanci tsakanin Jordan,Falasdinu,kasashen Gulf,da kuma Iraki.

A ranar 27 ga watan Oktoban shekarar 2018, Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya kai zai ziyara Umman,wacce ba ta da wata alakar diflomasiyya da kasarsa,inda ya gana da sarki Kabus Bin Said.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here