Hukumar Soji Ta Yi Tir Da Kalaman Gwamna Kashim Shettima

Win money on DrumbeatNews !!!

Ministan Tsaro, Mansur Dan-Ali da sauran jami’an tsaro ba su ji dadin furucin Gwamna Kashim Shettia ba na fifita wasu Janar na Soji a kan wadansu, har ya kai ga ambaton sunaye.

Gwamna cewa ya yi Janar Janar ‘yan Kudancin Najeriya wadanda kuma ba Musulmai ba, su ne musabbabin dawowar zaman lafiya a Borno. Ya kuma nuna cewar abokan aikin su Musulmai ‘yan Arewa ba su tabuka komai ba.

Ya kuma ce nasaran da a ka samu kan Boko Haram a makwanni 6 da su ka wuce, ya fi wanda a ka samu a shekaru 3 da su ka wuce. Har ma ya kai ga cewa sakacin wadansu kwamandoji a 2016 ne ya tayar da zaune tsaye.

DUBA WANNAN: Wani Likita Ya Saka Wa Mutane 40 Kwayar Cutar Kanjamau, Sun Shiga Wasan Buya Da Hukuma

Kwatakwata wannan furuci bai yi wa Hukumar Soji dadi ba don kuwa zagi ne da cin mutumcin sauran sojin da su ka sadaukar da rayukan su don samar da tsaro.

Da dama daga cikin Jami’an Sojin sun ce bai kamata irin wadannan kalamai na kabilanci ya fito daga bakin Gwamna ba. Jami’an sun kuma tunatar da Gwamnan cewar Hukumar Soji ba ta nuna bambanci ko kadan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here