Gwamnonin Arewa za su kori Ma’aikatan Makaranta a 2019 – El-Rufai

Win money on DrumbeatNews !!!

Mun samu labari cewa Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa Gwamnonin Jihohin Arewa za su sallami wasu bara-gurmin Malaman Makaranta idan su ka lashe zabe a 2019. Gwamna El-Rufai yace bai tsoron rasa kujerar sa Gwamna Malam Nasir El-Rufai yace Gwamnonin Arewan na gudun rasa kujerar su ne a zabe mai zuwa shi ya sa su ka gaza korar Ma’aikatan da ba su san aiki ba.

El-Rufai yayi wannan bayani ne lokacin da yake wani jawabi kwanan nan. Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa bayan zaben 2019 Gwamnonin Arewa da dama za su kori Malaman Makaranta kamar yadda yayi a Jihar Kaduna kwanakin baya.

Gwamnan na APC yace abin da su ka yin yayi daidai. KU KARANTA: Dangote zai kafa kamfanin kera motoci a Arewacin Najeriya El-Rufai yayi wannan jawabi ne a wata Makarantar koyon aikin Likita a Jihar Ondo. Gwamnan na Kaduna yake cewa Gwamnonin kasar da dama sun yaba masa bayan ya kori Malaman makaranta sama da 20, 000 da su ka fadi jarrabawa. Nasir El-Rufai ba ya jin tsoron daukar kowane irin mataki a Duniya idan har ya ga cewa shi ne abin da ya dace. Malam El-Rufai yace sauran Gwamnonin Kasar ba za su iya yin gangancin da yayi ba saboda gudun za su fadi zabe a 2019.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here