Gwamnatin Yobe Za Ta Sayo Motocin Naira Miliyan 245 Ga Jami’an Tsaro

Win money on DrumbeatNews !!!

A zaman da majalisar zartaswar Jihar Yobe ta gudanar karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam a shekaranjiya Laraba ta amince da ta kara sayo motoci samfurin Toyota Hilux (Akori kura) guda 14 a kan zunzurutun kudi har Naira Miliyan 245 ga jami’an tsaron Jihar da ke yaki da kungiyar Boko Haram. Da ya ke gabatar da jawabin bayan taron majalisar ga manema labarai a zauren taro dake ofishin kula da harkokin yada labarai a gidan Gwamnatin Jihar da ke garin Damaturu, kwamishinan ma’aikatar yada labarai da harkokin cikin gidan Jihar Alhaji Mala Musti ya jaddada cewar sayo wadannan motoci ga jami’an tsaro kari ne ga dimbin motocin da Gwamnatin ke saya ga jami’an tsaro don kawo zaman lafiya a Jihar.Kwamishinan ya ci gaba da cewar, kudirin Gwamna Gaidam ne akullum cewar ya ga zaman lafiya ya ci gaba da inganta a Jihar musamman ganin irin dagar da aka sha dangane da hare-haren ‘yan bindigar Boko Haram.

Baya ga wadannan motoci da Gwamnatin Jihar ta amince da sayo wa har ila yau, majalisar ta kuma amince Gwamnatin Jihar da ta gina gidajen saukar baki na musamman guda 3 a gidan Gwamnatin jihar masu dakunan kwana 4 kowannensu akan kudi Naira 126,714,147,00. Har wayau majalisar Zartaswar ta amince da Gwamnatin ta sayi babbanmasaukin bakin nan na GAAT HOTEL dake garin Damaturu akan kudi Naira Miliyan 578,161,010,43 don samarwa Jihar kudaden shiga.Alhaji Mala Musti ya kara da cewar majalisar zartarwar ta kuma amince Gwamnatin ta kashe kudade kimanin Naira Miliyan 369,910,405,71 don sake gyara babbar gadar nan dake kan hanyar Bara-Teteba da Gulani ganin cewar wannan gada tana da matukar muhimmanci ga al’ummomin yankunan.Ya kara da cewar majalisar ta kuma amince da Gwamnatin Jihar ta ginahanyar mota mai tsawon kilomita 2.23 hade da magudanun ruwa masu tsawon kilomita 4.46 akan zunzurutun kudi har Naira Miliyan 396,727,580,00 a rukunin gidajen Buhari Estate dake garin Damaturu. Da ya ke karin haske akan wadannan ayyuka kwamishinan ma’aiktar ayyuka da gidaje na Jihar Alhaji Lawan Shettima ya ce majalisar ta amince da hakan don ganin Gwamna Gaidam na da kyakkyawan kudiri da rayuwar al’ummar Jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here