Gwamnatin Tarayya Da Kamfanin Indiya Za Su Kafa Kamfanonin Casar Shinkafa A Jihohi 10

Win money on DrumbeatNews !!!

Gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan wata yarjejeniya ta dala bilyan 10.7 tare da kamfanin MB Agro Engineers Limited, domin kafa manyan kamfanonin Casar shinkafa a Jihohi goma na kasarnan. Ministan Ayyukan gona da raya karkara, Cif Audu Ogbeh, da takwararsa na kasar, Heineken Lokpobiri, suka sanya hannu tare da jami’an kamfanin na kasar Indiya jiya a Abuja. Jihohi 10 da za su ci gajiyar shirin sune, Anambra, Binuwe, Bayelsa, Bauci, Kebbi, Kaduna, Kogi, Neja, Ogun da Jihar Zamfara.

Za a baiwa Jihohin wuraren ne a kan bashi, wanda kuma za su biya shi a cikin shekaru goma. Ministan ya shaida wa manema labarai bayan bikin sanya hannun, cewa ma’aikatar na shi za ta yi wa Jihohi goman tallan kashi 10 na kudaden aikin. “Da zaran kamfanin ya iso, za su kafa injunan casar, daga nan kuma sai bankin manoma ya karbi ayyukan biyan bashin a cikin shekaru goma,” in ji Ministan. Ya kuma yi nuni da cewa, Dangote ya sayo sabbin injunan casar shinkafar guda goma, wadanda za su iya cashe tan milyan daya a duk shekara. Cif Audu Ogbeh ya ce, bayan wadannan da Dangote ya sayo, akwai kuma wasu kananan injunan casar guda 200, wadanda za su iya casan tsakanin tan goma zuwa ashirin, wadanda tuni an raba su a wuraren karkara na Jihohi 36 na kasarnan.

Tare da wannan sanya hannun da aka yi, ana sa ran kamfanin na MB Agro Engineers Pbt. Limited, zai kammala kafa injunan casar ne a cikin watanni 18, sai kamfanin ya ma yi alkawarin kammala kafa injunan a kasa da wannan lokacin da aka diban masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here