Gwamnatin Buhari na shirin ba tsohon kamfanin Atiku kwangila mai tsoka ta bayan-fage

Win money on DrumbeatNews !!!

Bincike ya nuna ana shirin a maida wa INTELS kwangilar tsaron jiragen ruwa.

A 2019 ne NPA ta karbe kwangilar gadin da aka ba kamfanin a tashoshin ruwa.

Alamu na nuna Minista ya dawo da INTELS cikin lissafi duk da bai cancanta ba.

Abuja – Gwamnatin tarayya ta na sake shirin ba kamfanin INTELS kwangilar shekaru 25 domin su rika sa ido a kan jiragen ruwa a tashoshin Najeriya.

Wani bincike na musamman da Daily Trust ta yi, ya nuna kokarin ba wannan kamfanin kwangilar duk da cewa an yi waje da shi tun wajen neman kwangilar.

A lokacin da za a bada kwangilar tsaron jirage a 2019, shugabar NPA ta lokacin, Hadiza Bala Usman ta rubuta wasika zuwa ga shugaban kasa, tayi karar INTEL.

Usman tace kamfanin ya saba ka’idar da aka yi da shi, don haka aka cire shi a cikin masu neman kwangilar. Hakan ya sa kamfanin ya shigar da kara a kotu.

Sauran kamfanonin da aka zaba cikin sama da 30 su yi takarar neman wannan kwangila ta biliyoyi sune; Pacific Silverline Ltd, da Isasha Investment Ltd.

Sai kuma kamfanonin ICA Logistics Ltd da wani Nexttee Oil & Gas Trading Company Ltd.

Source: Naija News

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here