Faransa na ci gaba da korar bakin haure daga kasar

Win money on DrumbeatNews !!!

Ministan Harkokin Cikin Gida na Faransa Christophe Castener ya bayyana cewar, ana ci gaba da korar bakin haure da suka shiga kasar ba bisa ka’ida ba.

Faransa na ci gaba da korar bakin haure daga kasar

Ministan Harkokin Cikin Gida na Faransa Christophe Castener ya bayyana cewar, ana ci gaba da korar bakin haure da suka shiga kasar ba bisa ka’ida ba.

Castener ya ce, a wannan shekarar an samu kari da kaso ashirin cikin dari na adadin mutanen da aka kora daga Faransa.

Ya ce, “A shekarar 2017 an samu kari da kaso sha hudu cikin dari na adadin wadanda aka kora, inda a wannan shekarar adadin ya akr da kaso ashirin.”

Minista Casterner ya kuma ce, ‘yan gudun hijira na tururuwa zuwa Faransa inda tun daga watan Oktoban 2017 aka samu karin mutane 200 a cibiyar da ake tsare wadanda aka kama.

Ofishin Kula da ‘Yan kasashen Waje na Faransa ya ce, an kori mutane dubu 14,816 daga kasar zuwa kasashen waje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here