Ebola ta salwantar da rayuka 942 a kasar Kongo

Win money on DrumbeatNews !!!

An bayyana cewar annobar cutar Ebola da ta bulla a kasar Jamhuriyyar Demokradiyyar Kongo (JDK) a watan Yulin bara ta yi sanadiyar rayuka 942 a kasar.

 

An bayyana cewar annobar cutar Ebola da ta bulla a kasar Jamhuriyyar Demokradiyyar Kongo (JDK) a watan Yulin bara ta yi sanadiyar rayuka 942 a kasar.

Alkaluma daga ma’aikatar lafiyar JDK sun bayyana cewar annobar da ta fara a jihar Arewacin Kivu ta kuma yadu a jihar Ituri an samu yawan wadanda ake ganin sun kamu da cutar da dubu daya da dari biyar da ashirin da tara.

Daga cikinsu an tabbatar da cewa mutane dubu daya da 463 na dauki da kwayar cutar Ebolan.

A cibiyar magance Ebola mutane 99 ne ake jinyarsu.

A yayinda cutar ta yi sanadiyar rayuka 942 mutane 422 na dauke da kwayar cutar a fadin kasar ta Kongo.

Haka kuma wasu da zazzabin da suke kuma fitar da jini su 66 sun rasu ana hasashen cutar ce sanadiyar rayukansu.

A ranar 8 ga watan Agusta 2018 da aka fara yaki da cutar an yiwa mutane dubu 110 da 803 rigakafin cutar.

Irin wannan cutar ta Ebola dai ta fara buluwa ne a duniya karon farko a shekarar 1976 a garin Nzara dake Sudan da kuma garin Yambuku dake kasar JDK.

Sabili da cutar ta fara bulla ne a wani kauye dake da rafi mai suna Rafin Ebola an radawa wannan cutar sunan rafin.

A watan Disambar shekarar 2013 ne cutar ta yada a kasashen Afirka ta Yamma.

An dai samu bulluwar cutar a kasashen Gini, Liberiya da Sierra Leone tsakanin shekarun 2014-2017. Cutar ta kama mutane dubu 30 inda kuma fiye da dubu 11 suka rasa rayukansu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here