Ebola ta kashe mutane 502 cikin watanni shida a Kongo

Win money on DrumbeatNews !!!

An bayyana cewar a cikin wata shidan da suka gabata yawan wadanda cutar Ebola ta kashe sun kai 502 a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.

Ebola ta kashe mutane 502 cikin watanni shida a Kongo

An bayyana cewar a cikin wata shidan da suka gabata yawan wadanda cutar Ebola ta kashe sun kai 502 a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.

Kamar yadda ma’aikatar lafiyar ƙasar ta fitar an warkar da mutane 271 a cikin watanni shida da suka gabata.

Ma’aikatar ta ƙara da cewa mutane 441 ne cutar ta kama inda 61 sunka riga mu gidan gaskiya a asibitocin da suke jinya.

Daga ranar 8 ga watan Agusta da aka fara kamfen ɗin yaki da cutar an yiwa mutane dubu 74 da 96 allurar riga-kafi.

Cutar Ebola ta fara bulluwa ne a shekarar 1976 a garin Nzara dake Sudan da kuma garin Yambuku dake Kongo a lokaci daya.

A shekarar 2013 cutar Ebola ta kara yaduwa zuwa kasashen Afirka ta yamma da suka hada da Gini, Sierra Leone da Liberiya. A tsakanin shekarun 2014-2017 kimanin mutane dubu 30 ne cutar da kama, inda mutane dubu 11 sunka rasa rayukansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here