Cavusoglu ya ce ila yanzu ba tsayayyiyar magana game da kafa yanki mai tsaro

Win money on DrumbeatNews !!!

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya ce “ila yanzu dai bamu ji abin da ya mana dadi ba game da kafa kebabben yanki mai tsaro a Arewacin Siriya ba”.

 

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya ce “ila yanzu dai bamu ji abin da ya mana dadi ba game da kafa kebabben yanki mai tsaro a Arewacin Siriya ba”.

A ziyarar da ya kai Amurka domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya na 74 ne Cavusoglu ya gana da ‘yan jaridan Turkiyya a birnin New York.

Bayan an masa wata tambaya game da kafa kebabben yanki mai tsaro ne ya ce asalin burin Turkiyya shi ne taga ta kori ‘yan ta’adda daga yankin inda ya cigaba da cewa,

“Amurka na da al’kawarin da ya kama ta cika a yankin. Burin mu shi ne mu kori ‘yan ta’adda domin kafa kebabben yanki, kuma haka ya sa za mu yi hadin gwiwa da Amurka da sauran kasashe amma ba mu taba hadin gwiwa da ‘yan YPG, PKK ko PYD ba. Sannan mu za mu taimaka wajen dawowar mutane bayan an kafa kebabben yankin”.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here