Boko Haram Ta Kashe Sojojin Chadi, Da Najeriya

Win money on DrumbeatNews !!!

kalla sojojin Chadi hudu da na Najeriya uku sun rasa rayukansu a wasu mabanbantan hare-haren da kungiyar Boko Haram ta kaddamar musu.

Boko Haram ta kashe sojin Chadi da wani dan jarida mai daukar hoto a harin da ta kai musu a wani sansani da ke yankin arewacin tafkin Chadi

Sai dai bayanai na cewa, sojojin na Chadi sun yi nasarar kashe ‘yan Boko Haram 23.

Sojin Najeriya kuwa sun rasa rayukansu ne a harin da kungiyar ta kai musu a sansanin garin Gubio mai tazarar kilomita 80 daga babban birnin Maiduguri na jihar Borno.

Maharan sun kai farmakin ne da yammacin jiya Asabar, inda suka yi lugudan wuta tare da fatattakar sojojin na Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here