Bincike: Mutane 1500 sunka rasa rayukansu cikin watanni 3 a Yaman

Win money on DrumbeatNews !!!

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar sanadiyar yakin basasar da ake yi a kasar Yaman tsakanin watan Agusta da Satumba zuwa Oktoba mutum 1500 sun rasa rayukansu.

 

Bincike: Mutane 1500 sunka rasa rayukansu cikin watanni 3 a Yaman

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar sanadiyar yakin basasar da ake yi a kasar Yaman tsakanin watan Agusta da Satumba zuwa Oktoba mutum 1500 sun rasa rayukansu.

Hakan na nuni da a cikin watanni 3 kachal an rasa mutane dubu 1500.

 

Mai magana da yawun hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Shabia Mantoo a taron da suka gudanar a Geneva ya bayyana cewar al’umar kasar yaman na cikin halin kakanikayi wadanda halin da suke ciki ke kara dagulewa a ko wacce rana, sabili da haka ya yi kira ga daukar matakan kare rayuwa da dukiyoyin al’umar kasar Yaman.

Malam Mantoo ya kara da cewa acikin watanni ukun da aka bayyana tashin-tashina har 670 da aka samu a kasar ya yi sanadiyar mutuwar ko raunanar mutane kusan dubu da 478 wadanda daga cikinsu 217 yara haka kuma 268 mata ne.

 

Mantoo, ya nanata cewa a cikin mako daya mutane 123 ke mutuwa a fadin kasar ta Yaman, inda ya kara da cewa daga ranar da aka fara yakin basasa a kasar mutane kusan mutane dubu 16 sunka rasa rayukansu.

 

An dai kwashe tsawon lokaci ana fafatawa tsakanin kungiyar Houthi da dakarun gwamnati sanadiyar riki da banbancin ra’ayin siyasa a kasar.

A yayinda kungiyar Houthi ta karbe ikon babban birnin kasar Sana a watan Satumbar shekarar 2014, ita kuwa dakarun da Saudiyya ke jagoranci ta fara kaddamar da hare-haren kalubalantar kungiyar Houthi a watan Maris din shekarar 2015.

 

A makon jiya ne dai majalisar dattawan Amurka ta fara sauraren ba’asi akan taimakawa Saudiyya da kasar Amurka ke yi a yakin da Saudiyyar ke jagoranci a Yaman.

Da yawan sanatocin na ganin cewa hanyar siyasa ita ce kadai tillo hanyar bi da za’a shawo kan rikicin kasar Yaman din cikin sauki da gaggawa.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here