Beraye sun zama annoba a New York

Win money on DrumbeatNews !!!

An bayyana cewar za’a fara amfani da wata sabuwar tarko mai barasa domin yaki da beraye a garin Brooklyn dake gundumar New York birni mafi girma a Amurka.

 

An bayyana cewar za’a fara amfani da wata sabuwar tarko mai barasa domin yaki da beraye a garin Brooklyn dake gundumar New York birni mafi girma a Amurka.

Magajin garin Brooklyn Eric Adams, ya gabatar da wannan sabon tarko mai suna “Ekomille” ga manema labarai.

Adams ya kara da cewa tarkon zai janyo baraye saboda abincin da aka sanya a samansa wanda da zarar sun hau zasu fada cikin bokiti mai cike da ruwan barasa.

Shugaban kanfanin Rat Trap Inc. da ya kirkiro  tarkon  Anthony Giaquinto ya bayyna cewar an yi amfani da wata nau’in giya da zata sanya berayen buguwa daga bisani kuma su nutse a ciki.

An bayyana cewar wannnan  tarkon ko wani dayansa zai iya kashe beraye 80 a rana. Ana dai yawan yin korafe-korafe akan beraye a birnin abinda ya zama tamkar annoba.

A binciken da jami’ar Columbia ta kudanar a shekarar 2014 ya nuna cewa akwai beraye fiye da miliyon biyu a garin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here