Bana nuna wariyar launin fata – shugaban kasar Amurka Donald Trump

Win money on DrumbeatNews !!!

Bayan ya sha kakkausar suka daga sassan duniya daban-daban a kan kalaman kasakanci da ya yi a kan kasashen nahiyar Afrika, shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewar shi ba mai nuna wariyar launin fata ba ne.

Trump ya bayyana haka ne a jiya Lahadi yayin da yake amsa tambayoyi kai tsaye a kan zarginsa da nuna wariyar launin fata, wannan shine karo na farko da shugaban ya taba amsa tambaya a kan wannan zargi da aka dade ana jifansa da shi.

Kafafen watsa labarai a kasar Amurka sun rawaito cewa, shugaban ya furta kalaman wulakancin ne kan Afrika a yayin ganawa da mambobin majalisar dokokin Amurka a ranar Alhamis kan batun shige da fice a kasar.

Shugaban ya bayyana kasashen Afrika a matsayin wulakantattun kasashe da suka gaza ta fuskar sama wa kansu cigaba.

Tuni kungiyar gamayyar kasashen afrika (AU) ta yi Alla-wadai da kalaman na shugaba Trump tare da fadawa shugaban ya gaggauta neman afuwar kasashen Afrika bisa kalaman cin fuska da ya yi a kansu.

ko a kwanakin baya saida Trump ya taba furta cewa ‘yan Najeriya basa kaunar komawa Afrika domin gudun komawa rayuwa a cikin bukka. Saidai shugaban ya gaggauta karyata yin wannan kalami.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here