Bana bukatar in canja kungiya: Messi ya mayarwa Ronaldo martani

Win money on DrumbeatNews !!!

 

Tauraron dan kwallon Barcelona, Lionel Messi ya mayarwa da abokin takararshi Cristiano Ronaldo martani akan gayyatar da ya mai ta cewa ya biyoshi kasar Italiya dan su ci gaba daga inda suka tsaya.

A makon da ya gabata ne Ronaldo da ya bar Real Madrid zuwa Juventus ya kalubalanci Messi da cewa, ya biyoshi Italiya su ci gaba da gasa, dan wasan yayi wannan ganane lokacin da aka tambayeshi ko yana kewar Messi? Yace, shi beyi kewar kowa ba yana farin ciki a inda yake Messin ne ma ya kamata ace yayi kewarshi dan shi a ko da yaushe yana son ya fuskanci sabon kalubale, yayi wasa a Ingila, sifani yanzu gashi a Italiya, yana kalubalantar Messin ya biyoshi su ci gaba, ya kara da cewa amma idan yana jin dadi a inda yake to yana girmama hakan.
Messin shi kuma yace, ba ya da bukatar canja kungiya, domin yana kungiyar da ta fi kowacce a Duniya kuma duk shekara yana fuskantar sabaon kalubale.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here