Babu Wanda Ya Isa Ya Hana A Rantsar Da Ni – Aminu Tambuwal

Win money on DrumbeatNews !!!

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi zargin cewa wasu na shirye shiryen haddasa rigingimun siyasa a jihar inda ya ce babu wanda ya isa ya hana a rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.

 

 

 

Gwamnan ya bayyana haka ta bakin babban hadiminsa, Alhaji Yusuf Dingyadi, inda ya ce wasu mutane suna yada kararraki da kuma haddasa rudani cewa kotu tana shirin tsige shi daga kujerarsa sannan ta mika mulkin ga APC.

Ya kara da cewa an cire fostan shi da aka lika a hanyar Birnin Kebbi, hanyar tashar jirgi da Maiduguri an kuma mayar da fostan dan takaran jam’iyyar APC.

Tambuwal ya karfafa cewa kotu kadai ce take da karfin hana gwamnatinsa.

 

 

 

Gwamnan ya shawarci jam’iyyar adawa da ta “bar kotu ta gudanar da aikin ta, jam’iyyar PDP a Sokoto bata nemi hukunci ta kofar baya ba. Kawai a bar kotu tayi abunda ya dace, muna da tabbaci akan kotu saboda mun lashe zabe ne da ikon Allah.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here