Ana shirin sabuwar zanga-zanga a Gaza

Win money on DrumbeatNews !!!

Al’ummar Falasdinawa na shirin gudanar da sabuwar zanga-zanga ranar Talata kwana guda bayan dakarun Israila sun kashe mutane 55 a Gaza. A ranar 15 ga watan Mayun ne kowace shekara ce ranar da Falasdinawa suka yiwa lakabi da Nakba, wato ranar da aka shaida mummunar bala’i . A ranar ce dubban jama’a suka fice daga gidajen su yayin da aka kafa Israila a shekarar 1948 wanda ke cika shekaru 70.

An dai fuskanci tashe tashen hankula ne sakamakon bude ofishin jakadanci Amurka a birnin Kudus. Jami’an Falasdinawa sun ce baya ga wadanda aka kashe akwai kimanin mutum 2,700 da suka samu raunuka a tarzomar. Ana kallon tarzomar a matsayin mafi muni a Gaza tun bayan yakin shekarar 2014.

Sauya wa ofishin matsuguni daga Tel Aviv dai ya yi matukar harzuka Falasdinawa wadanda ke kallon matakin da Amurka ta dauka a matsayin nuna goyon baya ga Israila na iko da birnin. Sai dai Firai ministan Israila Benjamin Netanyahu ya ce sojoji na kare kansu ne daga mayakan Hamas wanda ya ce suna son wargaza Israila. Tuni wasu kasashen duniya suka yi alla-wadai da kashe kashen inda Kuwait ta bayyana abun daya faru a matsayin babban abun takaici.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here