An saka dokar ta baci a kasar Cile

Win money on DrumbeatNews !!!

An dade ana zanga-zangar rashin amince wa da karin farashi a harkokin sadarwa a kasar Cile inda al’mura suka tabarbare a jiya har sai da aka shelanta dokar ta baci a jahohin Santiago da Chacabuco da kuma yankunan Puente Alto da San Bernardo.

An saka dokar ta baci a kasar Cile

An dade ana zanga-zangar rashin amince wa da karin farashi a harkokin sadarwa a kasar Cile inda al’mura suka tabarbare a jiya har sai da aka shelanta dokar ta baci a jahohin Santiago da Chacabuco da kuma yankunan Puente Alto da San Bernardo.

A wani jawabi da Firaministan Kasar Sebastian Pinera ya yi a Fadar La Moneda ne ya ce zanga-zangar na barazana ga zaman lafiyar mutane.

Mista Pinera ya cigaba da cewa, “harin da aka kai jirgin kasan Satiago da kuma sauran barna da aka yi a kasar ya sa ni, a matsayi na na Firaminista na shelanta dokar ta baci a jahohin Santiago da Chacabuco da kuma yankunan Puente Alto da San Bernardo.

Shugaban ya ce za a tattauna game da rage farashin a ranakun gaba.

Dokar ta bacin za ta kai kwanaki 15 tana gudana inda aka ce za a kara kwanaki 15 idan har ba shawo kan al’marin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here