An kashe ‘yan ta’adda 35 a Zamfara

Win money on DrumbeatNews !!!

A ranar Jumma’ar nan da ta gabata,rundunar sojojin Tarayyar Najeriya ta sanar da cewa, ta yi nasarar kashe ‘yan ta’adda 35, cafke 18 daga cikin tsagerun a raye da kuma kwato mutane 40 da aka yi garkuwa.

An kashe ‘yan ta’adda 35 a Zamfara

A ranar Jumma’ar nan da ta gabata,rundunar sojojin Tarayyar Najeriya ta sanar da cewa, ta yi nasarar kashe ‘yan ta’adda 35, cafke 18 daga cikin tsagerun a raye da kuma kwato mutane 40 da aka yi garkuwa.

Manjo Clement Abiade ya sanar da cewa,sun kaddamar da wasu gaggaruman farmakai.

Abiade ya ce,an kamo wasu ‘yan ta’adda 18 a raye tare da kwace makamai masu dumbin yawa da ke hannyensu.

Lokaci zuwa lokaci,  jihohin arewacin Tarayyar Najeriya na fama da kzaman rikice-rikicen da ke kunno kai tsa makiyiya da kuma manoma.

Manufar kabilun Fulani,wadanda makiyiya ne ita ce nema wa dabbobin abinci,abinda yasa a wasu lokuta, yayin da suke hijira zuwa yankunan kudancin Najeriya,manoma ke

yunkurin kai musu farmaki tare da kwace illahirin dabbobinsu.
Kungiyoyin ta’adda sun yi amfani da wannan babbar matsalat don cin karansu babu babbaka,inda suke garkuwa da mutanen da basu ji basu gani ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here