An kama sojojin da suka harbe ‘yar shekara 9 a Somalia.

Win money on DrumbeatNews !!!

Yan sanda sun ce an kama wasu sojoji hudu a Somaliya bayan da aka harbe wata ‘yar shekara tara a babban birnin kasar Mogadishu.
Kungiyar kare hakkin bil adama Amnesty International ta ce Deqa Dahir ta mutu, kuma wata yarinyar ta ji rauni lokacin da harsasai suka bula motar makarantar da ke dauke da su a cunkoson ababen hawa.
Kungiyar ta kara da cewa sojojin sun bude wuta a kokarinsu na bude wa motarsu hanya.
Shugaban Somaliya ya gana da iyalan Dahir, a yayin da jama’a ke nuna fushinsu kan harbin da aka yi.
An binne yarinyar a ranar Alhamis, kwana biyu bayan da aka kashe ta.
Yarinyar dai tana shekararta ta farko ne a makaranta, kuma tana kan hanyarta ta komawa gida ne cike da farin ciki, tana shan ayis kirim, a lokacin da aka harbe ta.
Harsashin ya same ta a kai ne inda ta mutu nan take.
Mahaifinta ya nemi gwamnatin Mohamed Abdullahi Mohamed ta bi masa hakkinsa.
Ya ce, “Na kadu matuka da na ga gawar ‘yata, na kasa cewa komai, ina bukatar adalci ga ‘yata,” in ji Dahir Moalim Ali Farah, kamar yadda ya shaidawa Amnesty.
“Ɗana mai shekara 11, wanda yake cikin motar makarantar tare da Deqa, ya zo gida yana kuka da ihu ya gaya mana cewa an harbe ta.
Sai na ruga zuwa wurin da abin ya faru, inda aka gaya mini an kai ta asibitin Masaarida,” in ji mahaifinta.
A wani al’amarin na daban kuma, harsashin da wani soja ya harba ya sami wani direban Keke Napep a ranar Litinin.
“Mayakan sa kai na Al-shabbab suna yawan dasa bama-bamai a Mogadishu, suna hakon mutanen da ke cikin cunkoson ababen hawa,” in ji Ahmed Adan.
Ya kara da cewar: “Saboda haka ba abun mamaki ba ne ka ga sojoji suna harbi kusa da fararen hula.”
Shugaban ‘yan sandan kasar Bashir Abdi Mohamed ya yi alkawarin cewa zai gurfanar da duk wanda ya yi harbin kan mai-uwa-da-wabi, kuma ya ce ana bincike a kan mutuwar yarinyar da aka kashe din.
Amnesty ta bukaci gwamnati da ta tabbatar da cewa dakaru sun daina amfani da karfi da wajen hulda da mutanen da suke harkokinsu na yau da kullum.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here