An gudanar da zaɓuka lamun lafiya a Libiya

Win money on DrumbeatNews !!!

Al’umman ƙasar Libya na gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a yankuna tara dake yammacin kasar karon farko bayan zaɓukan shekarar 2014.

 

An gudanar da zaɓuka lamun lafiya a Libiya

 

Al’umman ƙasar Libya na gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a yankuna tara dake yammacin kasar karon farko bayan zaɓukan shekarar 2014.

Kafar yaɗa labaran “Libya 24” ta rawaito cewa a rumfunar zaɓe 68 dake garuruwa tara a yammacin ƙasar ne dake ƙarƙashin Hukumar Haɗin Gwiwa UMH ake gudanar da zaben.

Shugaban hukumar zaben ƙananan hukumomin ƙasar Salim bin Tahiye ya bayyana cewar ba’a samu wata cikas ba a zaɓen.

Haka kuma hukumar ta bayyana cewar yawan wadanda suka fita jefa kuri’a ya kai kaso 40 cikin ɗari.

Hukumar bayar da tallafi ta Majalisar Ɗinkin Duniya dake Libya ta bayyana farin cikinta akan yadda aka gudanar da zaben ba tare da wata tsangwama ba, inda ta ƙara da cewa wannan alama ce ta ci gaban demokradiyyar da zaman lafiya a fadin ƙasar.

 

Ana dai sauraren sakamakon zaben daga hukumar zaɓen ƙasar wanda zata bayyana a cikin ƙanƙanen lokaci.

Ana kuma shirye-shiryen gudanar da zaɓuka a sauran yankunan ƙasar dake ƙarƙashin Hukumar haɗin gwiwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here