An Gano Cutar Kyandar Biri (Monkey Pox) A Jikin Wani Dan Nijeriya

Win money on DrumbeatNews !!!

Ma’aikatar kiwon lafiya na kasar Singapore ta gano cutar ‘Monkey Pox’ a jikin wani dan Nijeriya mai shekaru 38 da ya shigo kasar.

Sakamakon binciken da ma’aikatar ta gudanar ya nuna cewa wannan mutum ya kan yi muamula da nama daji a lokacin da yake Najeriya sannan daidai zai taho kasar Singapore din ya cicci naman daji da ake kyautata zaton anan ne ya kamu.

A yanzu haka wannan mutum na kebe a wani bangare a asibiti a na duba shi inda ma’aikatar ta kuma fara duba mutane 23 da suka yi muamula da wannan mutumi domin kada cutar ta yadu

A kwanakin baya Hukumar kula da kiwon lafiya ta kasar Britaniya (PHE) ta sanar cewa an gano cutar Monkey Pox a jikin wasu ‘yan Nijeriya biyu a kasar.

A dalilin haka shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka ta Nijeriya Chikwe Ihekweazu ya bayyana cewa hukumar za ta hada hannu da hukumar PHE don ganin an tarerayi cutar kafin ta yadu.

Shugaban hukumar PHE Nick Phin ya bayyyana cewa an fara gano wannan cuta ce a jikin wani dan Nijeriya a makon da ya gabata a asibitin ‘Cornwall’ sannan wannan makon ne aka gano na biyu din a asibitin ‘Blackpool Victoria’.

Phin yace bisa bincike cutar Monkey Pox ya bullo a Nijeriya tun a shekarar 2017 sannan zuwa Agustan 2018 mutanen da suka kamu sun kai 262 a jihohi na kasar inda kuma mutane 113 daga jihohi 16 suka rasu a dalilin kamuwa da cutar.

Karanta:: ‘Yan Bindiga Sun Wargaza Garuruwa Sama Da 98 A Jihar Zamfara

A karshe Ihekweazu ya ce NCDC za ta hada karfi fa karfe da kungiyar WHO, UNICEF da sauran kungiyoyin domin kawar da cutar a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here