An fara share gubar dalma a mujami’ar Faransa

Win money on DrumbeatNews !!!

Masu aikin sake gina mujami’ar Notre Dame ta birnin Paris na kasar Faransa sun soma aikin share gubar dalma a kewayen mujami’ar wadda gobara ta ci a watannin baya.

Yanzu haka an kafa shingaye a harabar mujami’ar da kewayenta, yayinda masu aikin sharar da manyan motoci ke ta wanke mujami’ar domin kakkabe gubar dalmar baki daya.

Tun bayan konewar mujami’ar a watan Afrilu, masana suka yi ta kashedin cewar,  gubar dalma za ta yi illa ga lafiyar al’ummar da ke makwabtaka da mujami’ar.

Za a yi amfani da na’urorin shara na zamani wajen aikin mujami’ar da aka kiyasta ya kai murabba’in mita 10 da 200, kuma ana sa ran kammala aikin kafin ranar 23 ga watan Agusta da muke ciki.

An dai tara miliyoyin Dala don sake gina mujami’ar ta Notre Dame mai dumbin tarihi, yayinda shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya sha alwashin sake gina ta nan da shekaru biyar masu zuwa.

AD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here