An damke sojojin Girka 2 da ke leke asirin Turkiyya

Win money on DrumbeatNews !!!

– An cafke wasu sojojin kasar Girka 2 wadanda suka tsalake iyakar Turkiyya da nufin leken asiri.

– Ankara, ta yi Allah wadai da bayanan da Girka ta yi game da sojojinta 2 da ke garkame a Turkiyya.

A cewar wata sanawar da ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ta fitar, jawabin da hukumomin Girka suka yi a baya bayan nan kan batun sojojinsu 2 da aka cafke a ranar 1 ga watan Maris na bana a yankin Erdinen Turkiyya, na kara nuna cewa,Girka na ci gaba da furta munanan lafuzzan ga Turkiyya,inda ya ce,

“Sanin kowa ne,idan ita ke da gaskiya Girka sai ta dinka tunkaho da bugun gaba tare da da’awar doka ta yi halinta,amma da zaran ba ita ce ke da gaskiya ba, sai ta yi kunnen uwar shegu ta hanyar yin wasa da hankali da hujjoji, kana ta dinka jan kafa wajen aiki da doka.Muna bakin cikin shaida wadannan halayen da ba su dace da  kasar da ta san yakamata ba”.

A ranar 1 ga watan Maris shekarar 2018, jami’an tsaro na kan iyakan Turkiyya sun damke wani Leftana da saja na wata rundunar sojan Girka da ke leken asiri a gaf da yankin Pazarkule,inda bayan an kwace bindigogin da ke hannunsu aka mika su ga hedkwatar jandarmomin Erdine.

An kama sojojin wadanda daga bisani aka gurfanar da su gaban kotu da laifin tsalake iyaka ba bisa ka’ida ba da kuma gudanar da aiyukan leken asiri,inda a dalilin haka.

Kotu ta yanke shawarar tisa keyar leftana Aggelos Mitretodis da na saja Dimitros Kouklatzis gidan wakafi.

A bayanan da masu laifin suka yi, sun tabbatar da cewa sahun kafafunsu ne da sojojin Turkiyya suka bi suka yi amfani dasu wajen kama su, kana bidiyoyi da hotunan da aka gani a wayoyinsu, sun dauke su da nufin aika wa manya da kuma shugabanninsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here