Al-Makura ya sallami dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar Nasarawa

Win money on DrumbeatNews !!!

Al-Makura ya sanar da sallamar masu rike da mukaman siyasar ne yayin taron majalisar zartarwa na jihar da aka gudanar a ranar Laraba a Lafia babban birnin jihar. Ya ce ya dauki matakin ne domin saukaka mika mulki zuwa ga zababen gwamnan jihar Mr Abdullahi Sule.

 

Sai dai Al-Makura ya ce wasu daga cikin jami’an gwamnatin na sa masu rike da muhimman makamai za su cigaba da ayyukansu har zuwa ranar 29 ga watan Mayu. Ya kuma umurci dukkan kwamishinoninsa su tattara rahotanninsu na aiki su mika masa kafin ranar 20 ga watan Mayu. Gwamnan ya ce rahotannin za su taimakawa wadanda za su gaje su. Ya ce bayan sun mika rahotannin ayyukansu dukkan kwamishinonin za su cigaba da kasancewa a ofisoshinsu har zuwa ranar 29 ga watan Mayu. “Tare muka zo kuma tare za mu tafi. “Za muyi aiki tukuru domin tabbatar da cewa mun mika mulki ga gwamnati mai zuwa ba tare da cikas ba,” inji Al-Makura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here