Abubwa 10 dazakuyi domin kaucewa cututtuka yayin Ambaliya.

Win money on DrumbeatNews !!!

A yanzu haka ‘yan Najeriya da dama na fama da ambaliyar ruwa a jihohi daban-daban na kasar inda mutane da dama suka rasa rayukansu wasu kuma suka rabu da muhallansu.
Wannan ya biyo bayan gargadin da hukumomi suka yi ne a kasar cewar za a yi ambaliyar ruwa a jihohi 13 cikin kasar, musamman wuraren da ke kusa da kogin Kwara da na Binuwe.
Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (CDC) ta bayar da wasu shawarwari goma da za su taimaka wa jama’a wajen kauce wa cutar kwalera a lokacin ambaliyar.

1.Kada ku sha ruwan ambaliya ko kuma ku yi amfani da shi wajen wanke-wanke ko wanke baki ko kuma sarrafa abinci.
2.Ya kamata al’ummu su tabbatar da sun saka sinadarin Chlorin na kashe kwayoyin halittu a hanyoyin samun ruwansu.
3.A tabbatar da cewa an zubar da shara yadda ya dace tare da gyara magudanar ruwa.
4.A rinka wanke hannaye a da sabulu da ruwa sau da yawa.
5.A zubar da dukkan magunguna da abinci da ruwan kwalba da ruwan ambaliya ya bata.
6.A cikin gidaje kuwa, a tabbatar cewa an tafasa ruwa da kyau kafin a sha.
7.A kaurace wa bahaya a fili tare da zubar da shara ba bisa ka’ida ba.
8.A gujuje wa cizon sauro ta hanyar tabbatar da cewa ana amfani da raga mai dauke da maganin sauro.
9.Ma’aikatan kiwon lafiya su dauki matakan riga-kafi a kowane lokaci.
10.Idan kuka kamu da zazzabi da zawayi cikin lokaci kadan, ku garzaya cibiyar kiwon lafiya na take

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here