Abbas ya kara neman goyon bayan kasashen Afirka

Win money on DrumbeatNews !!!

Shugaban kasar Falasdinu Mahmud Abbas ya bayyana cewar bawai ga Falasdinu ba, ba kuma ga Venezuela ba, ba zamu bayar da dama ga wata kasa mai suna Amurka ta yi katsalandan ga ko wacce kasa ba a fadin duniya.

 

mahmud abbas afrika birligi.jpg

Shugaban kasar Falasdinu Mahmud Abbas ya bayyana cewar bawai ga Falasdinu ba, ba kuma ga Venezuela ba, ba zamu bayar da dama ga wata kasa mai suna Amurka ta yi katsalandan ga ko wacce kasa ba a fadin duniya.

Abbas,ya yi wannan kiran ne a yayinda yake jawabi a gaban Majalisar Tarayyar Kasashen Afirka a helkwatan hukumar dake Addis Ababa babban birnin kasar Ethiopia.

Shugaba Abbas ya godewa shugaban tarayyar akan ire-iren gudunmowar da suka baiwa kasar ta Falasdinu. Inda ya kara da cewa ya zama wajibi “Mu ci gaba da hadakar dake tsakaninmu”

Abbas ya kara da cewa Isra’ila wacce ke ci gaba da daukar matakan canja al’adun Kudus na kara daukar matakan da suka sabawa dokokin kasa da kasa tare da goyon bayan da take samu daga Amurka.

Ya kara da cewa Falasdin na dukkanin kokarin ganin an samar da maslaha ta kasa biyu, inda ya kara da cewa Amurka bata da wata guri ko katabus akan lamurkan kasar Falasdin.

Abbas, ya jaddada cewa ba ga Falasdin ba, ba kuma ga venezuela ba, ba zamu yarda da ko wacce irin kalubale ba a kasashen mu ba.

A yayinda Abbas ke sukar yunkurin mayar da ofishin jakadancin Amurka ta Isra’ila daga Tel Aviv zuwa Kudus, ya yi kira da kasashen Afirka da karsu mayar da ofisoshin jakadancinsu zuwa Kudus.

Isra’ila daga shekarar 2002 na yawan rokon goyon bayan kasashen nahiyar domin cimma burinta.

Shugaban kasar Falasdin wanda kasarsa ke mambar sa ido a tarayyar na halartar taron kolin tarayyar a ko wani lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here