Ƴan ƙungiyar Taliban sun kashe ƴan sanda 3 a wata hari da suka kai Afghanistan

Win money on DrumbeatNews !!!

Ƴan ƙungiyar Taliban sun kashe ƴan sanda uku a wani hari da suka kai a garin Jaguri dake jihar Gazne na ƙasar Afghanistan.

Ƴan ƙungiyar Taliban sun kashe ƴan sanda 3 a wata hari da suka kai Afghanistan

Ƴan ƙungiyar Taliban sun kashe ƴan sanda uku a wani hari da suka kai a garin Jaguri dake jihar Gazne na ƙasar Afghanistan.

Mai magana da yawun magajin jihar Jaguri Muhammed Aref Nuri ya bayyana cewar an kashe ƴan kungiyar Taliban 5 tare da raunana wasu da dama a lokacin da suka kai hari a jihar.

Nuri, ya ƙara da cewa tuni da jami’an tsaron yankin sun fatattaki mambobin kungiyar Taliban daga yankunan.

A ɗayan barayin kuma mai  magana da yawun kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya bayyana cewar sun kashe jami’an tsaro 25 a yankunan bincike 9 da ƴan sanda ke gudanarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here